Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutane 89 bisa zargin aikata laifuka daban-daban, wannan na matsayi kokarin hukumar na magance ayyukan bata gari a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya,
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a shelkwatar rundunar dake Bompai, Kano a ranar Litinin.
Dogo ya ce laifukan da mutanen suka aikata sun hada da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Read Also:
Ya ce, an yi kamen ne a wurare daban daban na jihar, daga ranar 12 ga watan Satumba zuwa yau inda ya kara da cewa an mika mutane 53 da ake zargi gaban kotu a yayin da 36 ake kan bincike a kansu.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin SP, Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar, ya ce an kwato makamai masu hatsari daga wajen wadanda ake zargin da suka hada da bindiga da adda da wukake.
Sannan ya ce rundunar za ta ci gaba da aiwatar da aikin ta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
“A don haka, rundunar ‘yansanda zata ci gaba da sauke nauyin dake kanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada”, inji Kwamishinan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 9 minutes 57 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 51 minutes 22 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com