Home AFIRKA Fasinja 78 sun mutu bayan nutsewar jirgin ruwan da suke ciki a...

Fasinja 78 sun mutu bayan nutsewar jirgin ruwan da suke ciki a Congo

Aƙalla mutane 78 ake fargabar sun rasa rayukansu a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo bayan nutsewar wani jirgin ruwa yayin da yake ƙoƙarin ketara tabkin Kivu ɗauke da fasinjoji 278.

Gwamnan Lardin Kudancin Kivu da ke gabashin Jamhuriyar Congon Jean Jacques ne ya tabbatar da adadin mamatan na mutane 78, da kuma yawan fasinjojin kusan 300 da ke cikin jirgin da ya nutse.

Sai dai ya ce basu kammala tantance adadin rayukan da suka salwanta a haɗarin ba, aikin da ya ce zai ɗauki jami’an ceto aƙalla kwanaki uku suna yi.

Har zuwa daren jiya dai an riƙa samun bayanai masu cin karo da juna akan yawan waɗanda haɗarin jirgin ruwan ya rutsa da su, domin a yayin da mahukuntan lardin Kivu suka bayar da nasu alƙaluman, takwarorinsu na arewacin Lardin Kivun cewa suka yi mutane 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 58 suka tsira.

Ɗaukar fasinjoji fiye da kima ke kan gaba a cikin dalilan dake haddasa yawaitar nutsewar jiragen ruwa a Jamhuriyar Congo, lamarin da ake kyautata zaton ko a wannan karon shi ne musababbin haɗarin da ya auku.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp