Home Labarai An hallaka manoma huɗu a wani hari a Filato

An hallaka manoma huɗu a wani hari a Filato

'Yan Ta'adda

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wasu manoma huɗu tare da jikkata wasu biyar a wani hari da aka sake kai wa wurin hakar ma’adinai kusa da kauyukan Kuba da Maikatako da ke karamar hukumar Bokkos na jihar Filato.

Shugaban matasan yankin Butura, Sabastine Majit, shi ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos ranar Asabar, inda ya ce an kai harin ne da misalin karfe na dare ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa maharan sun tsere bayan kai harin, kafin isar jami’an tsaro.

“Wanna hari ya zo ne kwanaki huɗu bayan wani mummunan hari a kauyen Wumat, inda aka kashe mutum biyar ƴan gida ɗaya, ciki har da wata mata mai ciki,” in ji Sabastine.

Ya ce wannan hari shi ne na baya-bayan nan da ake kai wa al’ummomin yankin, wanda ya janyo mutuwar mutum 20 a cikin wata ɗaya kaɗai.

Ya ƙara da cewa wannan na cikin hare-hare da yawa da ake kai wa ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom da Bassa da Jos ta Arewa da kuma ta Kudu da Wase da kuma Mangu a baya-bayan nan, inda ake kashe mutane.

Sai dai babu wani ƙarin bayani daga rundunar ƴansandan jihar ta Filato kan wannan hari da aka kai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp