Ƴan bindiga sun harbi babban kwamandan dakarun sa kai na jihar Zamfara

Afghan military personnel walk near the airport during fighting between Taliban militants and Afghan security forces in Kunduz on October 1, 2015. Afghan forces pushed into the centre of Kunduz on October 1, triggering pitched gunfights as they sought to flush out Taliban insurgents who held the northern city for three days in a stinging blow to the country's NATO-trained military The stunning fall of the provincial capital, even temporarily, highlighted the stubborn insurgency's potential to expand beyond its rural strongholds in the south of the country Afghan forces, hindered by the slow arrival of reinforcements but backed by NATO special forces and US air support, struggled to regain control of the city after three days of heavy fighting. AFP PHOTO / Wakil Kohsar

A Wata musayar wuta da aka yi a tsakanin ƴan bindiga da dakarun tsaro na sakai CPG a jihar Zamfara dake Arewacin Najeriya, ƴan ta’addar sun kashe mutane dama inda suka raunata wasu cki har da babban kwamandan rundunar ƴan sa kan Janar Lawal B. Muhammad mai ritaya.

Rahotanni dai sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar Funtua zuwa Tsafe ne mai cike da cunkoson jama’a da yammacin ranar lahadi, inda suka far wa masu ababen hawa ciki har da Darakta janar na hukumar ta CPG.

Sannan a yayin wannan samamen ƴan bindigar sun yi  awun gaba da wasu fasinjoji da dama dake kan hanyarsu ta zuwa wurare daban-daban.

Wata majiya daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Zamfara, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce shugaban na samun kulawa a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar.

Wannan arin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ‘yan bindiga suka kashe jami’an na CPG akalla takwas da wani direban motar  sufuri a karamar hukumar Tsafe da ke jihar ta Zamfara.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi wa jami’an na CPG kwanton bauna ne kafin su an kara suka bude musu wuta.

Da yake bayani game da harin, babban kwamandan da aka harba ya bayyana cewa, bayan da ya fahimci cewa ‘yan bindigar na shirin kai hari a tsafe, sai ya tura jami’an CPG 105 zuwa karamar hukumar tare da ajiye su a wannan wuri domin baiwa matafiya kariya ba tare da sanin sun musu riga Malam masallaci ba.

Sai gashi abin bakin ciki ƴan bindigar sukai musu kwanton bauna saboda sun kwana a wurin, a yayin da dakarun sa kan suke sauka sai suka bude musu wuta kuma suka kashe wasu daga cikinsu tare da jikkata wasu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 35 minutes 10 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 16 minutes 35 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com