Home General Fashewar tankar mai ta kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa

Fashewar tankar mai ta kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa

Wata tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya bayan ta faɗi tare da kamawa da wuta.

Babbar jami’ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa’adu, ta ce zuwa yanzu mutum 104 ne suka mutu sakamakon hatsarin da ya faru ranar Talata da dare.

Da take magana yayin da ta isa wurin da lamarin ya faru a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura, Aisha ta ce wasu mutum 100 sun jikkata.

Tun da farko ta ce ibtila’in ya faru ne bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.

Hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.

Kakakin rundunar ‘yansanda a Jigawa, DSP Lawan Adam, ya ce ganin haka ne ya sa mutane suka yi dafifi a wurin da lamarin ya faru domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami’an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.

Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

Zuwa yanzu ana shirin yin jana’izar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar.

Hotunan da aka turo wa BBC sun nuna yadda aka lulluɓe gawarwakin mutanen da ganyayyaki, yayin da wasu hotunan suke ɗauke da gawarwakin da suka rasa wasu sassa na jikinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp