Majalisar dattawa ta ƙasar Kenya ta tsige matamakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua.
Shugaban majalisar ya ce sanatoci sun tabbatar da tuhume-tuhume biyar daga cikin 11 da aka gabatar a kan tsohon mataimakin shugaban ƙasar, waɗanda duka ya ƙaryata.
Daga cikin laifukan akwai raba kan al’umma da saɓa dokokin aikin ofis ɗinsa da kawo tsaiko a aikin tattara bayanan sirrin ƙasar.
Rigathi Gachagua mai shekara 59 ya yi iya bakin ƙokarinsa domin hana tsigewar, sannan ko a yammacin alhamis lauyansa ya ce ba zai samu halartar zaman majalisar ba saboda yana kwance a asibiti, har ya buƙaci a ɗage zaman, amma sanatocin suka ƙi amincewa, inda suka cigaba da tattaunawa ba tare da yana nan ba, har suka kai ga tsige shi.
Sai dai yana da damar ƙalubalantar tsigewar a kotu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 49 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 30 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com