Home Labarai Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta Kama Dan Sandan Bogi a jihar

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta Kama Dan Sandan Bogi a jihar

Rundunar  ‘yan sandna jihar kano ta sami nasarar kama wani matashi da take zargin da yin sojan gona, matsayin dan sandan bodi a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Wannan na cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar na kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar aka rabawa manema labarai a jihar a daren Alhamis, inda ya ce sun kama shi ne biyo bayan koken da al’umma suke yi a Kansa.

A cewar Kiyawa, “Mun kama wani matashin Salisu Bala mazaunin unguwar Kurna, a sakamakon yadda yake sojan gona da kakin ‘Yan Sanda yana karbar kudi a hannun al’umma da sunan shi Dan Sandan Sarauniya ne”.

Kuma dai yana gudanar da wannan aika-aikar tasa ne a unguwannin Sabon Gari, Fagge, Koki dake kwaryar birnin Kano.

To sai dai bayan kamo shi da aka yi bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, CP Salman Dogo Garba, an gano kayan ‘Yan Sanda hudu a gidansa, a inda daga bisani ya tabbatar da cewa yana ta’ammali da kayan maye.

domin haka ne CP Dogo Garba ya ce ba zasu dagawa masu aikata sojan gona da sunan rundunar ko kuma ‘Yan Sandan Sarauniya ba domin haka rundunar ta bayar da wannan lambar waya (07038188127), domin al’umma su shigar da korafi akan ‘Yan Sandan dake musguna musu.

A karshe rundunar ta kuma bada lambobin wayar da za’a bada rahoton dukkan wani abu da ba’a gamsu da shi ba, 08032419754, 08123821575.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp