Home Labarai ‘Yan Nijeriya zasu fara samun isasshiyar wutar Lantarki nan da shekaru 5

‘Yan Nijeriya zasu fara samun isasshiyar wutar Lantarki nan da shekaru 5

Gwamnatin Nijeriya ta ce kasashen Togo da Benin yanzu haka Nijeriya na basu wutar lanatarki na tsahon sa’oi 24 ko wacce rana.

Manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na Hukumar Rarraba wutar lantarkin Najeriya TCN, Sule Abdulaziz  ne ya bayyana hakan ta cikin wata tattaunawa da kafar yada labarai ta Channels TV a ranar lahadi inda ya ce ƙasashen Togo da Benin suna samun wutar lantarki ta sa’a 24 daga Najeriya.

“Muna ba Togo da Benin da Nijar lantarki. Suna samun wutar awa 24, kuma suna biya,”

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ƴan Najeriya da dama ba sa samun wutar kamar haka, sai ya ce, “Yan Najeriya na samun wuta sosai amma ba a ko’ina ba. Waɗanda suke Band A suna samun lantarki na tsakanin awa 20 zuwa 22 a rana,” in ji shi.

Abdulaziz ya ƙara da cewa, “ina tabbatar muku za mu iya fara samun isasshiyar wutar lantarki nan da shekara biyar. Sabon ministan yana ƙoƙari domin tabbatar da hakan.”

Ya ƙara da cewa akwai bambanci tsakanin TCN da Nepa, “lokacin da muke Nepa, mu ne muke samar da wutar, mu rarraba, sannan mu yi kasuwancinta, amma yanzu rarraba wutar kawai muke yi,” in ji shi. Sannan ya ƙara da cewa idan aka samu tangarɗa daga babban layin ƙasar, ana ɗora musu laifi ne saboda ana musu kallon Nepa.

“Idan an samu tangarɗa ba dole ta zama daga TCN ba, domin za a iya samu a sauran ɓangarorin.”

Shugaban na TCN ya kuma bayyana lalacewar kayan aiki, a matsayin wata matsala da ke addabarsu, inda ya ce, “yawancin kayayyakin aikin da muke amfani da su sun haura shekara 50.”

A game da tsadar lantarki kuwa, Abdulaziz ya ce, wutar lantarki na da sauƙi a Najeriya, idan aka kwatanta da wasu ƙasashen Afirka irin su Burkina Faso da Senegal da Jamhuriyar Nijar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp