Jami’an hukumar hana fasa kwauri a jihar Kebbi sun sami nasarar kama fatar jaki 180 da ake yunƙurin yin fasa-ƙwaurinta.
Kwamandan rundunar a jihar Kebbi, Iheanacho Ojike, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce sauran kayaki da suka kwace sun haɗa da litar man fetur har guda 16,300 da tufafi da kuma katan-katan guda 74 na wasu magunduna daban-daban wanda kuɗin fitonsu ya kai sama da naira miliyan 300.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Iheanacho ya ce an yi samu nasarar kama kayan ne bisa irin ƙoƙari da jami’an hukumar suke yi wajen kakkaɓe masu aikata ɓarna.
Kwamandan hukumar ya ce wasu mutane na amfani da lokacin tsadar man fetur wajen safararsa zuwa waje.
Ya ƙara da cewa an kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a fasa kwaurin kayakin.
Ya kuma gargaɗi masu fasa kwauri da su daina domin jami’ansu a shirye suke wajen cafke su.












