EU da Jamus sun bai wa Najeriya tallafin kusan yuro miliyan 18

Kungiyar tarayyar turai da ƙasar Jamus sun ƙaddamar da kaso na 3 na shirin tallafawa Najeriya dangane da abinda ya shafi makamashi NESP domin habbaka sabbin hanyoyin samar da isashshen makamashi musamman a yankunan karkara.

Shirin zai laƙume kuɗin da ya kusa yuro miliyan 18 inda za a sada mutane 1,500 da lantarki da kuma samarwa da mutane dubu 30 gas na girki.

Har wa yau a kashi na 3 na wannan shirin za a samar da wutar lantarki mai ƙarfin Megawatts 8.

Tallafin na samar da makamashi ga Najeriya an fara ƙaddamar da shi tun a shekarar 2013 wanda kungiyar tarayyar turai EU da tallafin ƙasar Jamus haɗin gwiwa da ma’aikatar lantarki ta Najeiya.

Kungiyar ta tarayyar turai ta amince ta ƙara zuba kuɗi a kashi na 3 na wannan shiri domin taimakawa ci gaban da kuma samar da tsarin lantarki ta sabbin hanyoyin makamashi da kuma tabbatar da jama’a sun amafana da shirin.

Mataimakin Ambasadan ƙasar Jamus Johannes Lenhre ya tabbatar da shiri ƙasarsa wurin cimma muradan da Najeriya ta snaya a gaba a fannin makamashi.

Sakataran ma’aikatar lantarki a Najeriya Mahmuda Mamman ya yaba da irin tallafin da Najeriya ke samu daga kungiyar tarayyar turai da Jamus musamman yadda suke ƙoƙarin tabbatar da samun isashshen makamashi a ƙasar

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 25 minutes 4 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 6 minutes 29 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com