MDD ta yi gargaɗin samun matsananciyar yunwa a Najeriya a 2025

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, mai lura da al’amuran jin ƙai ya yi hasashen samun matsananciyar yunwa a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.

Cikin wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi gargaɗin samun tsanantar matsalar a Najeriya tsakanin watan Nuwamban 2024 zuwa watan Mayun 2025.

”Ya kamata a ɗauki matakai domin yaƙi da yunwa da ceto rayukan mutane a yanzu da kuma tsawon lokaci a nan gaba”, kamar yadda ofishin ya wallafa.

Bayanan da ofishin ya fitar sun nuna cewa a NAjeriya, mutum miliyan 38 ne za su fuskanci matsalar, yayin da ƙasar Sudan ta Kudu ke biye mata da mutum miliyan 21, sai ƙasar Ethiopia mai mutum miliyan 15.

A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin Najeriya ta sanar da wasu matakai uku na kawo sauƙi ga matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.

Ɗaya daga cikin matakan shi ne, gwamnatin ta fito da tan 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma da nufin kawo sauƙi ga al’ummar ƙasar.

Haka kuma gwamnatin ta ce idan har matsalar ta faskara za ta iya ɗaukar matakin shigar da abinci daga ƙasashen waje domin magance tsadar abinci a faɗin ƙasar.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 8 hours 32 minutes 2 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 13 minutes 27 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com