Home General Gwamnatin jihar Kano za ta fara rijistar baƙi

Gwamnatin jihar Kano za ta fara rijistar baƙi

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yiwa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci.

Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, ta yadda za a haɓɓaka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin Kano, zai tattara bayanan baƙi ƴan ƙasashen waje da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma’aikata ko kuma kasuwanci.

Shugaban kwamitin, Lawan Isa Kibiya ya ce aikin da za su yi zai taimaka wajen tabbatar da ganin baƙin waɗanda mafi yawa ƴan kasuwa ne su na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi.

Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa gwamnati ƙwarin gwiwar ‘‘ƙoƙarin ganin ta samar da yadda za ta ba su kariya ta fuskar tsaro’’

Kwamishinan ma’aikatar ciniki ta jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya wanda manba ne a kwamtin ya ce ‘‘aikin bai taƙaita ga buƙatar tattara haraji kaɗai ba, duk duniya akwai ƙa’idoji da aka kafa a doka, waɗanda idan baƙo ya je zai yi kasuwanci ga ƙa’idojin da ya kamata ya bi, sannan su ma ƴan gari ga ƙa’idojin da ya kamata su bi.’’

Ya ƙara da cewa ‘‘idan ka shiga wannan manyan kasuwannin namu, musamman kantin kwari, za ka ga baƙin su ne mafi yawa ke ƙerawa, su yi packaging su kuma yi kasuwanci kai tsaye.’’

Adamu Kibiya, ya kara da cewa ire-iren waɗannan abubuwan gwamnati ta kalla shi yasa ake ƙoƙarin fito da tsarin da zai taimaki al’umma musamman wajen samar da ayyuka da kare martabar kasuwanci: ‘‘Idan muka zura ido mu ka yi gaba to zai zamo nan gaba mun koma maula, mutanen mu sun koma bara. Don haka gwmanati ta duba, ta ga dole wannan abubuwa a taka masu birki.’’

Ya ƙara da cewa tsarin zai tsaftace harkokin kasuwanci a jihar, musamman yadda aka saba samun masu yi wa ƴan kasuwa zambo domin kwashe masu kuɗi, kuma ana samun irin waɗannan bata gari masu aikata daga kowanne ɓangare.

‘‘Za ka ga ana karɓar kayansu da yawa ana cinyewa, kuma su ma daga cikin su ana samun masu cinye wa ƴan kasuwar Kano kaya ko kuɗinsu, to gwamnati ta ga cewa dole ta shiga tsakani domin a kawo kyakkyawan yanayi na kasuwanci’’

Kwamitin dai ya tabbatar da cewa rijistar ba ta shafi ƴan wasu jihohin da suke zaune a jihar Kano ba, sannan kwamitin ya kunshi jami’an tsaro na ƴan sanda da DSS da hukumar kula da shige da fice da ƴan kasuwa da kuma shugabannin kungiyar ƴan China masu kasuwanci a jihar Kano, inda ake fatan nan da makonni biyar kwamitin ya mikawa gwamnati rahotansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp