Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa, TCN, ya bayyana cewa bata-gari sun lalata layin wuta mai karfin 33KV daga Lokoja zuwa Gwagwalada.
Wannan na kunshe ta cikin wa sanarwa da Manajan yaɗa labarai na kamfanin, Ndidi Mbah, ta fitar a ranar Lahadi, wadda tace ɓatagarin sun lalata rumbun raba wutar lantarki na T306, T307 da kuma T308 a ranar Asabar.
Ta ce sun kuma sace wayoyin alminiyon har dauri biyu.
Read Also:
A cewar Ndidi, an gano hakan ne bayan da TCN ya tashi ma’aikatan sa don gano musabbabin katsewar wutar lantarki da safiyar Asabar.
Sai dai ta ce an fara kokarin gyaran matsalar, inda ta baiwa al’ummar yankin da ma sauran da ke kan layin wutar hakuri.
Matsalar wutar lantarki ta sha na daga cikin matsaloli na baya bayannan dake jifa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali da asarar dukiya mai tarin yawa.
PRNigeria Hausa











