Ministan kwadagon Kasar Saidou Zainabu ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ta Kira rana juma’a da ta wuce a birnin Yamai.
Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta ce ta bankado ma’aiktan bogi sama da dubu 3 wadanda ake biya albashin miliyan 540 kowane wata cikin asusun gwamnati.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Zainabu ,ta ce wani bincike da aka gudanar tsakanin watan Yuli zuwa Augustan wanan shakara ya gano yadda ake zurare biliyoyin kudi daga asusun bital malun na kasa domin biyan ma’aikatan da babu su a zahiri.
Rahoton binciken ya ce a watani uku farkon shekara 2022 biliyan 7,7 aka kashe wajan biyan fanshon ma’aikata sabanin biliyan 12,8 da aka kashe a watanin uku farkon shekara 2023 duk da raguwa masu tafiya ritaya da aka samu saka makon tsawaita lokacin zuwa ritaya da akayi da shekaru 5.











