Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana wajen shirya taron jin ra’ayin jama’a kan sabon ƙudirin harajin ƙasar da ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.
A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin karatu na biyu, inda kuma yanzu ta miƙa shi ga kwamitin kuɗi na majalisar domin shirya taron jin ra’ayin jama’a kan ƙudurin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ce kan ‘yan ƙasa ya haɗu wajen yin kira a samar da tsare-tsaren kuɗi bisa adalci da daidaito ga kowane yanki.
”Mun faɗa da babbar murya cewa bai kamata tsare-tsaren kuɗi da gwamnatin ƙasar ke son ingantawa su fifita wasu jihohin ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba”, in ji Atiku Abubakar.
”A matsayina na mai ruwa da tsaki, na yi imanin cewa gaskiya da adalci da riƙon amana da kyakkyawan shugabanci, na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi”.
Majalisar dattawan ƙasar ta ce ta amince da ƙudirin ne a karatu na biyu domin bayar da dama a shirya sauraron ra’ayin jama’a a kansa.












