Home General Ina neman afuwa kan goyon bayan ƙudurorin haraji – Kofa

Ina neman afuwa kan goyon bayan ƙudurorin haraji – Kofa

Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar Ƙiru da Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ba ɗari bisa ɗari yake goyon bayan ƙudurorin gyara haraji ba, sannan ya ƙara da cewa yana bayar da haƙuri.

Kofa ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba, inda a ciki ya ce, “babu wurin da ko sau ɗaya na ce ina goyon bayan sababbin dokokin haraji ɗari bisa ɗari.”

A cewarsa, “Abin da na ce (shi ne) akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga yankin arewa da ma Najeriya. Kuma mu ƴan majalisa na yankin arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a majalisa mu yi tsayin-daka mu goyi bayan duk wasu ƙudurorin da za su amfani arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankinmu da suke cikin kudurorin. Sannan mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su ta yadda ba za su cutar da mu ba.”

A cikin rubutun ya ƙara da cewa yana so ne yankin arewa su yi amfani damar dokar wajen bijiro da wasu sabbin hanyoyi, “mu shigar da su a cikin kundin ƙudirorin,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, “ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata ko Arewa da ma Najeriya ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp