Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NIMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo da kura a sassan Najeriya daga yau Litinin zuwa Laraba.
Hukumar ta ce yankunan Arewacin dama na tsakiyar Najeriya ne za su fi fuskantar yanayin na hazo da da kura.
NIMET, ta ce za a samu matsala wajen hangen nesa saboda hazon a tsawon kwanakin ukun.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Daga nan hukumar ta bukaci jama’ar da ke zaune yankunan da hazon zai fi tsanani da su dauki matakan kariya musamman wadanda ke fama da wata lalura data shafi rashin kura ko hazo kamar Asma ko kuma cutukan da suka shafi numfashi.
Kazlaika NIMET, ya shawarci kamfanonin jiragen sama da ke zirga-zirga a Najeriya da su tabbata sun samu cikakken rahoton game da yanayin da za a iya kasancewa da shi a iya kwanakin da aka hasashen fuskantar hazo da kurar.











