Home General Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello

Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.

A zaman da kotun ta yi a yau Juma’a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.

Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kotun ta ce dole ne masu tsaya masan su gabatar wakotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.

A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.

Lamarin da ya sa kotun ta tura shi gidan gyaran hali, a yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar.

Sai dai Yahaya Bello ya musanta aikata ba daidai ba.

Mai shari’a Nwite ya ce dole ne tsohon gwamnan ya ajiye wa fasfo ɗinsa n tafiye-tafiye.

Haka kuma ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da zai cika sharuɗan beli.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai babbar kotun Abuja ta tura tsohon gwamnan gidan yarin Kuje bayan fatali da buƙatar belinsa kan zarge-zargen karkartar da sama da naira biliyan 100 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp