Home General Akwai yiwuwar ƙara kuɗin kira da na data a sabuwar shekarar 2025...

Akwai yiwuwar ƙara kuɗin kira da na data a sabuwar shekarar 2025 a Najeriya

Akwai yuwuwar kamfanonin sadarwa a Najeriya su samu amincewar hukumar da ke kula da su NCC domin su ƙara kuɗin data da na kiran waya a sabuwar shekarar 2025.

Wani babban jami’i da ya nemi a sakaya sunanshi ya ce hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ka iya bai wa kamfanonin damar ƙara kuɗi.

Dailytrust ta rawaito cewa dukda tsadar rayuwa ammaanƙi amincewa kamfanonin su ƙara kuɗin kira sama da shekaru 11 da suka gabata.

Kamfanoni kamar MTN da Airtel da 9Mobile sun jima suna miƙa buƙatar ƙarin kuɗin GA Hukumar duba da yanayin tattalin arziki a ƙasar.

Wasu majiyoyin kamfanonin sadarwar sun ce ƙarin da za a fuskanta a ƙasar zai iya kaiwa kaso 40.

Wannan na nufin cewa kiran waya na minti 1 zai tashi daga naira 11 zuwa 15.40, aika sakon kar ta kwana a salula zai tashi daga naira 4 zuwa naira 5.60.

Farashin data 1GB zai tashi daga naira dubu 1 zuwa dubu1 da 400

A ranar 20 ga watan disamba a wata tattaunawa da manema labarai ministan sadarwa na Najeriya Dr. Bosun Tijani ya nuna cewar akwai buƙatar sake duba farashin.

A shekarar 2023 ne kamfanin MTN yayi asarar da ta kai Naira biliyan 137, asarar da ta ƙaru zuwa biliyan 514.9 a watanni 9 na farkon 2024.

Kamfanin Airtel dake aiki a Afrika shima ya sanar da yin asarar da ta kai dala miliyan 89 a 2024 kuma hakan ya biyo ƙaluabalen da yake fuskanta a Najeriya

Kawo lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin da abin ya shafa a Najeriya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp