Home General Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zarge-zargen shugaban mulkin sojin Nijar

Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata zarge-zargen shugaban mulkin sojin Nijar

Gwamnatin Najeriya ta ce zargin da shugaban mulkin Sojin Nijar Abdourahmane Tchiani ya yi cewa ƙasar na ƙoƙarin haɗa kai da Faransa wurin kawo hargitsi ba shi da tushe ballantana makama.

Ministan yaɗa labarai na Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wata takadda da ya fitar a yammacin yau a matsayin martani kan wata hira da shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar Tchiani ya yi. inda ya zargi Najeriya da ƙoƙarin kawowa ƙasar tsaiko.

Sanarwar ta ce shugaban Najeriya Bola Tinubu a mtsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ya nuna shugabanci abin koyi tare da barin ƙofa a buɗe ga Jamhuriyar Nijar duk kuwa da halin da ake ciki na juyin mulki a ƙasar.

Najeriya ta ce a shirye take wurin tabbatar da kyakykyawar alaƙa da zaman lafiya da fahimtar juna da kuma kyautata alaƙar diflomasiyya mai tsohon tarihi dake tsakaninta da Nijar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sojin Najeriya haɗin gwiwa da abokanan hulɗarta na samun nasara sosai wurin yaƙi da ta’addanci a yankin, don haka abin mamaki ne ace ƙasar za ta haɗa kai da wata ƙasar waje wurin kawo tsaiko ko rashin zaman lafiya a makwaftan ƙasashe.

Gwamnatin Najeriyar ta ce babu wani jami’inta da ya taɓa goyan bayan ƙungiyoyin ƴan ta’adda ko wata kungiyar ƴan ta’adda wurin kaiwa Nijar hari.

Gwamnatin ƙasar ta ce Najeriya ta tsaye kan kafafunta da cikakken iko kan ƙasar. kuma ba ta taɓa bai wa wata ƙasa dama ko iko na kafa sansanin soji a cikinta ba, sabanin abin da wasu ƙasashe ke yi. Wannan na nuna yadda shugabancin Najeriya ya yi tsayuwar daka wurin tabbatar da  ƴancin ƙasar.

Dangane da zargin da shugaban ƙasar Nijar ya yi cewa ana shirin kawowa bututun mansu da ayyukan gona tazgaro  gwamnatin ta ce kwata-kwata ba gaskiya bane.

Gwamnatin Najeriya ta ce waɗannan zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani ya yi tamkar kawar da hankalin jama’a ne kan gazawar da mulkinsa ya yi tun bayan da ya jagoranci juyin mulki. inda gwamnatin ta buƙaci da Jamhuriyar Nijar ta mayar da hankali wurin tattaunawa da haɗa kai maimakon zarge-zarge marasa tushe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp