Home General Murar Tsuntsaye: An buƙaci Al’ummar Kano su Kwantar da Hankalinsu

Murar Tsuntsaye: An buƙaci Al’ummar Kano su Kwantar da Hankalinsu

Gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani zargi da ake da shi game da cutar murar tsuntsaye ga hukumomin da abin ya shafa.

Wannan dai na kunshe ta cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Lafiya ta jihar Ibrahim Abdullahi ya aikewa PRNigeria, wadda ta ce biyo bayan raɗe-raɗin ɓullar annobar sakamakon wani rahoton da aka samu a watan Disamba na 2024 cewa wani matashi ɗan ƙaramar hukumar Gwale ya sayo agwagwa a kasuwar Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa ya haɗa ta da kajin da yake kiwo.

Daga baya sai ya lura kajin sun fara nuna alamun matsalar numfashi da har ta kai 35 cikin 50 sun mutu. Hakan ya sa ya kai wasu daga cikin waɗanda suka mutu asibitin dabbobi na Gwale domin yin bincike, inda a makon farko na watan Janairun 2025 sakamakon binciken ya nuna murar tsuntsaye ce ta yi sanadin mutuwar tasu.

Samun sakamakon binciken ke da wuya, sai ma’aikatar noma ta je ta kulle wurin da mutumin ke yin kiwon tare da kashe ragowar kajin da yi wa wurin baki ɗaya feshin magani. Haka kuma, ma’aikatar ta yi irin wannan feshin a wurin da ake sayar da kaji a kasuwar Janguza tare da wayar wa masu sana’ar kai game da illar murar tsuntsaye.

saboda hakan ne yasa, Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, a cikin sanarwar, ya buƙaci jama’ar jihar kano dake ARewa maso yammacin Nijeriya da su kwantar da hankalinsu saboda lamarin bai kai a kira shi ɓarkewar annoba ba.

Kwamishinan ya ce ma’aikatar lafiya na tsaye sosai a kan al’amarin, tana da ɗaukar dukkan matakan da suka dace na tunkarar matsalar domin daƙile tasirinta kafin ta zama barazana.

Dakta Labaran ya ce kasancewar cutar murar tsuntsaye na harbar mutum tare da haddasa illa ga jiki ya sanya ya kira taro da kwamitocin Kar-ta-Kwana da na Lafiya Guda Ɗaya (Emergency Preparedness Response da One Health) da ke da wakilcin ma’aikatun noma, muhalli da albarkatun ruwa da kuma ƙungiyoyin ci-gaba domin a tattauna tare da tsara hanyoyin da za a tunkari al’amarin.

Ya ce, “Wannan shi muke yi a halin yanzu. Za a rinƙa yin taro da masu ruwa da tsaki a kowane mako. Za a rinƙa sanar da al’umma a kai a kai halin da ake ci game da cutar.

“Za a ƙarfafa sa ido a kowace ƙaramar hukuma, musamman tsakanin masu kiwon kaji da sauran tsuntsaye, sannan za a rinƙa bai wa waɗannan kwamitoci rahoto a kowace rana tare da sanar da Gwamna Abba Kabir Yusuf halin da ake ciki.”

Kwamishinan ya ce alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, fitar da majina, jan-ido da sauransu, inda ya buƙaci al’umma musamman masu kiwon kaji da su zama jami’an sa ido na farko saboda su kare ababen da suke kiwo da dukiyoyinsu, tare da kai rahoton duk wani yanayi da ke hana kajin walwala ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki a kan lokaci.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp