Home General Mun samar wa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 10 a 2024 – NNPCL

Mun samar wa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 10 a 2024 – NNPCL

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya ce ya zuwa watan Satumban shekarar 2024, kuɗin da ya samar wa gwamnatin tarayya ya kai naira tiriliyan 100.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya sanar da hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kuɗi na majalisar dattawa, inda yake kare kasafin kuɗin kamfanin na bana.

Ya ce NNPCL na fitar da bayanan asusunsa na shekara-shekara, “Hada-hadarmu a fili suke, kuma muna bayyana duk harkokin kuɗin da muka yi a fili ba tare da nuƙu-nuƙu ba,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kyari ya ce kamfanin na NNPCL ne kamfanin da ya fi biyan haraji, kuma wanda ya fi samar da riba ga masu zuba jari.

Sai dai ya ce sai sun zauna tare da daraktocin kamfanin ne za su iya fitar da hasashen kuɗin da za su samar a bana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp