Home General Ana Fargabar Mutane Da Yawa Sun Mutu A Gobarar Tankar Mai A...

Ana Fargabar Mutane Da Yawa Sun Mutu A Gobarar Tankar Mai A Naija

Ana fargabar mutane da dama sun rasu wasu kuma sun jikkata, a yayin da suke kokarin dibar man fetur daga wata tankar mai da ta fadi a kwanar Dikko da ke babban titin Abuja zuwa Kaduna, a jihar Naija.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar, a lokacin da tankar da ke gudu ta fadi man ya zube, mutane suka je suna kwasar man sai motar ta yi bindiga wuta ta tashi.

Wutar ta kone mutane da dama da ke kwasar man yayin da wadanda suke nesa da ita kuwa suka ji rauni.

Kakakin gwamnan jihar Naija, Bologi Ibrahim, ya tabbatar wa da Emergency Digest faruwar lamarin, harma ya ce Gwamnan jihar Mohammed Bago, ya nuna alhininsa a kan Iftila’in.

A karshe ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da tsaro a wajen, sannan sauran hukumomin gwamnatin jihar su yi abin da ya wajaba a kai.

Ko a watan Oktobar shekarar da ta wuce an sami makamancin wannan Iftila’i a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa, inda sama da mutum 170 suka mutu, baya ga jikkatar sama da 50, a sakamakon fashewar tankar, lokacin da wasun su ke kwasar mai.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp