Dakarun Najeriya da suke aikin soji na musamman Fansan Yamma sun ce sun kashe ƴandinga da dama, ciki har da ɗan cikin Turji a wani samame da suka kai a sansanin ɗanbindigar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hedkwatar taron Najeriya, Edward Buba ya fitar, inda ya ce, “a ranar 17 ga Janairu, dakarun Fansan Yamma sun kutsa dazukan da ke yankin Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da Chindo, inda suka kashe gomman ƴanbindiga, sannan suka kashe ɗan cikin Bello Turji a Fakai, inda yake ɓoyewa.”
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun samu ƙashe ƴanbindiga da dama, da ɓarnata ma’ajiyarsu, “sannan sun ceto wasu waɗanda Bello Turji ya yi garkuwa da su, bayan ya tsere.”
Sanarta ta ce sojojin sun kai wani samamen a sansanin wani ɗanbindigar mai suna Idi Mallam, “inda sojoji suka kashe ƴanbindiga 3, da kama mutum 3 da ake zargi da taimakon ƴanbindiga, tare da ƙwato wasu makamai da dabbobin da suka sace.”
A ƙarshe Buba ya ce sojojin za su cigaba da fatattarkar ƴanbindigar a ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.










