Home General Alamu na nuna yiwuwar Najeriya za ta ga ƙarancin mahajjata a bana

Alamu na nuna yiwuwar Najeriya za ta ga ƙarancin mahajjata a bana

Alƙaluma na nuna yiwuwar Najeriya ta fuskanci ƙarancin maniyyata a hajjin bana, wanda ke da nasaba da hauhawar farashin kujerar hajjin bisa bayanan da hukumar kula da aikin hajji ta ƙasar NAHCON ta fitar a rana Litinin.

Hankula sun tashi matuƙa bayan da hukumar aikin hajjin Najeriyar ta fitar da farashin kujerar ta bana wanda ya tasamma miliyan 8 da rabi a wasu yankunan har ya zarta hakan.

Dai dai lokacin da ya rage ƙasa da wata guda kan wa’adin da NAHCON ta bayar wajen kammala biyan kudin aikin hajjin na bana, har yanzu ana ganin ƙarancin mutanen da ke miƙa kuɗinsu don sayen kujerun aikin hajjin na bana wanda alƙaluman ke nuna yiwuwar ya iya zama hajji mafi ƙarancin jama’a daga Najeriyar.

Alƙaluman farashin da NAHCON ta fitar ya nuna cewa mahajjata daga kudancin ƙasar za su biya tsabar kudi har naira miliyan 8 da dubu 700 yayinda maniyyata da arewa maso gabashin Najeriya kuma za su biya naira miliyan 8 da dubu 300 a gefe guda mahajjata daga arewaci kuma za su biya naira miliyan 8 da dubu 400.

Shugaban hukumar ta NAHCON farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa hukumar ta yi aiki tuƙuru wajen ganin farashin hajjin a bana bai kai naira miliyan 9 ba.

A baya dai an yi fargabar farashin aikin hajjin a bana ya iya kai naira miliyan 10 musamman lura da karyewar darajar takardar kudi ta Najeriyar naira.

Ƙarƙashin dokokin hukumar NAHCON dai dukkanin maniyyacin da ya gaza biyan adadin kudin aikin hajjin kafin nan da ranar 5 ga watan Fabarairu kai tsaye sai dai ya jira zuwa shekara mai zuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp