Home General Najeriya ta buƙaci zama mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Najeriya ta buƙaci zama mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Najeriya ta bukatar kasancewar ta mamba a hukumar sulhu ta Majalisar Ɗinkin Duniya a yayi taron duba lamuran tattalin arziki na duniya wato DAVOS 2025 wanda ke gudana a Switzeland.

Ministan harkokin Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ne ya nuna buƙatar ganin Najeriya ta kasance cikikkaiyar mamba ta hukumar sulhi ta Majalisa Ɗinkin Duniya, a yayin da yake bayyana tasirin ƙasar ke dashi wajen wakiltar nahiyar Afika a hukumar.

Da yake jawabi a yayin wani taron tattaunawa mai taken “tasirin Afika” a taron duba tattalin arzikin duniya da aka yi a birnin Davos na kasar Sweden a ranar 21 ga watan Janairun 2025, ministan ya koka ga  kwamitin sulhu ta MDD bisa rashin Afirka a cikin hukumar, yayin da yake bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na kudurorin majalisar sun shafi batutuwa masu alaka da Afirka.

Ya kuma yi nuni da cewa, da yawa daga cikin dokokin da Majalisar ta fitar na da illa ga nahiyar ta Afirka, ciki har da dokar sare dazuzzuka, wadda ta haramta sayen amfanin gona daga yankunan da aka sare dazuka, tare da yin watsi da kamfanonin fasaha da ke kera na’urorin da ke ba da damar sare dazuka a nahiyar.

Tuggar ya ƙara da cewa, ƙarƙashin mulkin shugaban Najeriya Bola Tinubu Kasar ta samu ingantuwar lamura kuma duniya ta shaida.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp