Home General Novak Djokovic ya fice daga gasar cin kofin Davis da Serbia

Novak Djokovic ya fice daga gasar cin kofin Davis da Serbia

Mai lamba ta 6 a duniya Novak Djokovic ya fice daga gasar cin kofin Davis da Serbia za ta buga da Denmark sakamakon rauni a kafarsa

Rauni ya tilasta Djokovic, mai shekaru 37, ficewa a wasan kusa da na karshe na gasar Australian Open da Alexander Zverev na Jamus a makon jiya saboda raunin da ya samu, inda magoya bayansa a Melbourne suka yi masa ihu.

Zakaran na Grand Slam na sau 24 ya saka hoton gwajin MRI da aka yi masa a kafarsa ta hagu a shafukan sada zumunta inda ya rubuta cewa ya saka wannan ne domin masana raunin ƴan wasa su gani domin tabbatar da yanayin da ya sa shi ya fice daga gasar.

Serbia, wacce za ta yi rashin Djokovic, za ta kara da Denmark a wasan share fage na zagayen farko, wanda za a fara ranar Juma’a 31 ga watan Janairu.

Kyaftin din Serbia Viktor Troicki ya ce sun samu rauni na rashin Novak, amma har yanzu suna da ƙwarin gwiwar samun nasara.

Denmark suna da babban dan wasa, wato Holger Rune, amma ‘yan wasansu ma suna da kyau kuma ya yi imani da tawagarsu.

Tawagar Serbia yanzu ta ƙunshi Miomir Kecmanovic, Hamad Mededovic, da Laslo Dere, da kuma ƙwararrun ƴan double ‘yan’uwan Sabanov, Matej da Ivan.

Haka kuma Serbia za ta kasance ba tare da Dusan Lajovic ba saboda rauni.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp