Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi naira dubu 25 ga duk wanda aka samu da laifin tofar da yawu ko majina akan titunan birnin Kano.
Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta amince da ita na tabbatar da tsaftar Muhalli ta cikin shirin ayyukan gyara birnin Kano da kawatashi domin samar da birni mai cike da tsafta a Najeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano kuma dan majalisar Dala Hon. Lawan Husaini wanda ya yi wa manema labarai karin bayani, inda ya ce wajibi ne gwamnatin kano ta dauki matakan da suka dace wajen tsaftace birnin Kano, domin dawo da martabar birnin a idanun duniya.
Dan majalisar yace abin kunya ne da takaici yadda wasu ke yawan tofar da yawu ko face majina akan hanya duk lokacin da suka ga dama.
wakilin mu na zauren majalisar jihar kano ya ruwaito mana cewa majalisar tayi Karatu na biyu akan yiwa hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli garambawul.
Daga cikin gyaran dokar hukumar ta kwashe shara harda, bukatar samar da cikakken Mataimakin hukumar da kuma bata cikakkiyar dama ta aikinta yadda ya kamata.











