Kungiyar kwadago ta janye zanga Zangar da ta shirya gudanar wa a Talatar nan sakamakon Karin kudin kiran waya da na Data.
Wannan ya biyo bayan wata ganawa da ta yi da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnatin tarayya a daren Litinin, kungiyar kwadagon ta ce ta yanke shawarar dakatar da zanga-zangar har sai an dawo teburin tattaunawa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero, ya ce gwamnati ta amince da kafa wani babban kwamiti da zai duba daukacin tsarin kudin Kiran waya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cewarsa, kwamitin zai kunshi wakilai biyar daga bangarorin biyu kuma ana sa ran zai mika rahoton bincikensa cikin makonni biyu.
Ya kara da cewa kungiyar za ta dauki matakan zanga-zanga da yajin aiki nan gaba, mutukar ba’a Sami wata matsaya ba kan rahoton Kwamitin .
Idan za,a iya tunawa dai a makonnin da Suka gabata ne hukumar Sadarwa ta kasa ta amincewa kamfanonin sadarwa masu zaman kanau da su kara kashi Hamsin na kudin Kiran waya da na amfani da data, wacce ta Kai ga kungiyar kwadago barazanar fita zanga zanga a ranar hudu ga watan Fabarairu.











