Wata babbar kotu da ke Kano a Najeriya ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar ratay bayan kama su da laifin kisan wata tsohuwa bisa zargin maita.
Kotun ta ce ta samu mutanen da laifin yin silar mutuwar tsohuwar mai shekara 67 a duniya a ranar 15 ga watan Nuwamban 2023, ba tare da ƙwaƙƙwarar hujja ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A lokacin yanke hukuncin, mai shari’a Usman Na’abba ya bayyana cewa kotun ta samu hujjoji ƙarara da suka tabbatar da laifin waɗanda ake tuhuma.
Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke ƙaramar hukumar Wudil ta jihar Kano.
Maita da tsafi abubuwa ne da ke yawan janyo cece-ku-ce a ƙasashen Afirka, inda iyalai kan ɗauki mataki kan mutanen da suke zarga da sanadin kashe musamman yara ta hanyar maita.











