Home General Sarki Dutsen ya Zama Uban Jami’ar Al-Istiqama

Sarki Dutsen ya Zama Uban Jami’ar Al-Istiqama

Jami’ar Al-istiqama da ke garin Sumaila ta nada sabon Sarkin Dutse Alhaji Muhammad Hamim Sunusi a matsayin sabon chancilor.

Naɗin nasa wanda ya gudana a masarautar Dutse a yau Alhamis 6 ga watan Fabrairu 2024, na zuwa ne biyo bayan karewar wa’adin Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Da yake miƙa takardar naɗin mamallakin Jami’ar Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdulraman Kawu Sumaila, ya bayyana daɗaɗɗiyar alaƙarsu da masarautar Dutse, wanda hakan ya sanya hukumar gudanarwa jami’ar taga dacewar baiwa Mai martaba Sarkin Dutse dama domin zama Chancellor na Jami’ar, duba da yadda masautar ke baiwa addinin musulunci muhimmanci matuƙa dai dai da yadda aka ɗora manufar gudanar da Jami’ar.

Da yake jawabi mai martaba sarkin Dutse Alhaji Muhammad Hamim Nuhu Sunusi, ya nuna jin daɗinsa bisa karrama masarautar tare da godewa wanda ya assasa jami’ar da sauran hukumomin gudanarwarta.

Ya kuma ƙara da cewa tun abaya sun san za’azo wannan gaɓa duba da irin alaƙa ta mutunci da girmanawa dake tsakanin masarautar da yankin Sumaila.

Sarkin ya kuma yi alƙawarin bada gudunmawar masauatar ɗari bisa ɗari domin ci gaban wannan jami’a dama al’umma baki ɗaya.

Zuwa yanzu dai jami’ar ta samu sahalewar gudanarwa na din-din-din daga hukumar dake kula da jami’o’i ta ƙasa NUC bayan tsallake zangon gwaji da jami’ar tayi na tsawon shekaru.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp