Home General Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Tinubu ya dauke Aminu Ado daga gidan...

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Tinubu ya dauke Aminu Ado daga gidan Nassarawa

Gwamnatin jihar kano ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauke sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero daga jihar kano domin samar da masalaha a jihar, la’akari da yadda wasu ke amfani dawannan damar wajen neman tayar da husuma a fadin jihar .

Mataimakin gwamnan jihar kano kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan, inda yace zaunar da sarkin kano na 15 a gidan sarkin na Nassarawa anyi shi da wata niya domin hana gwamnatin kano ta zauna lafiya da kuma kin yiwa al’ummar jihar abin da ya dace.

Freedom Radio ta rawaito kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo yace zanga-zanga da al’umma su ka fito a wannan satin, al’umma suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so.

Haka kuma suna da damar su nemi a cire sarkin kano na sha biyar daga gidan Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga cikinsu.

Gwarzo ya kuma ce suna kira ga shugaban kasa da ya gaggauta dauke sarkin kano na sha biyar daga cikin jihar Kano domin barin al’umma su zauna lafiya.

Gwamnatin kano ta ce yadda doka ta kawo tsohon sarkin haka doka ce ta kawo sabon sarkin dan haka abar doka ta yi aiki

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp