Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da hukuncin kotun ƙolin ƙasar, bayan ta yi cikakken nazarin takardun hukuncin.
Yayin wani jawabi da ya gabatar wa ƴan jihar a ranar Lahadi, Mista Fubara ya ce gwamnatinsa za ta bai wa hukumar zaɓen jihar haɗin kai wajen sake shirya wani zaɓen ƙananan hukumomin, bayan kotun ta rushe wanda aka yi a shekarar da ta gabata
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A ranar Juma’a kotun ƙolin ƙasar ta rushe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar 5 ga watan Oktoban 2024.
Gwamnan ya kuma umarci duka shugabbanin ƙananan hukumomin su miƙa ragamar gudanar da ƙananan hukumomin ga daraktocin mulki na ƙananan hukukomin a gobe Litinin 3 ga wata.
Ya kuma bayyana aniyar naɗa shugabannin riƙo har zuwa lokacin da za a sake gudanar da wani sabon zaɓen.











