Home General Tinubu ya nada sabon Akanta Janar a Nijeriya

Tinubu ya nada sabon Akanta Janar a Nijeriya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi, a matsayin sabon Akanta Janar na ƙasar.

Mashawarcin shugaban ƙasar kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Boyo Onanuga ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, inda ya ce shugaban ya naɗa shi ne bayan an tantance shi.

Nadin nasa, wanda aka amince da shi a yau, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da wanda yake kan mukamin Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya.

Sanarwar ta ce sai da shugaba Tinubu ya sa aka bi matakai daban-daban, wajen tantance Ogunjimi mai shekaru 57 domin tabbatar da ƙwarewarsa.

Ogunjimi ya kammala karatunsa na digirin farko a Jami’ar Nsukka, a shekarar 1990, inda ya karanci harkar akanta, sannan kuma ya sami digiri na biyu a fannin tsumi (Accounting) a Jami’ar Legas, a inda yanzu haka Mamba ne a Cibiyar Akantoci ta Najeriya.

A ƙarshe Tinubu ya buƙace shi da ya dage wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na yi wa Najeriya hidima cikin gaskiya, ƙwarewa, da sadaukarwa ga hidimar ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp