Home General Ƴanbindiga sun kashe ƴan sa-kai 13 a jihar Kebbi

Ƴanbindiga sun kashe ƴan sa-kai 13 a jihar Kebbi

Rahotanni daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa kimanin mutum 20 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ƴan bindiga suka kai a wasu garuruwa biyu a jiya Lahadi.

Lamarin ya faru ne a yankin karamar Hukumar Augie – ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.

Koda yake kawo yanzu ba a tabbatar ko su wa ne maharan ba.

Wani ɗan jarida Jameel Gulma dake a yankin ya bibiyi labarin, inda ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ƴan sa-kai suka bi su.

“A nan suka yi wa ƴan sa-kan kwantan ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.”

jihar ta Kebbi  na guda cikin jihohin arewacin Nijeriya dake fama da matsalar rashin tsaro, musamman na ‘yan bindiga dake satar mutane domin karbar kudin fansa wanda ke sake jifa jihar cikin halin na durkushewar tattalin arziki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp