Home General Najeriya za ta samar da lantarki ta hasken rana ga wasu jihohin...

Najeriya za ta samar da lantarki ta hasken rana ga wasu jihohin arewa 19

Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirinta na gina tashoshin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin megawatt 1,900 ga jihohin arewa 19, a wani bangare na ƙoƙarin bunkasa makamashin mara gurbata muhalli da kuma faɗaɗa cibiyoyin samar da lantarki ta ƙasa

Ministan Wutar Lantarkin Najeriya, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai karo na shida na 2025 da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, inda ya bayyana burin gwamnati na samar da kusan MW 8,000 na wutar lantarki kafin ƙarshen wa’adin mulkin Shugaba Bola Tinubu na farko a shekarar 2027.

Adelabu ya ce kowace tasha mai amfani da hasken rana za ta samar da kusan megawatt 100 na wutar lantarki, wanda hakan zai baiwa jihohi damar dogaro da kai da kuma rage dogaro da babbar cibiyar samar da wutar lantarki ta ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na bin diddigin samun masu saka hannun jari masu zaman kansu don taimakawa wajen faɗaɗa babbar cibiyar lantarki ta ƙasa tare zamanantar da ita.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ƴan Najeriya ke nuna damuwa dangane da yadda babbar cibiyar samar da lantarki ta ƙasa ke lalacewa tare da jefa ƙasa baki ɗaya cikin dubu a baya-bayan nan, musaman yankin arewa da ya fuskanci kalubale ta hanyar katsawar lantaki da aka alakanta da bata gari da ke lalata turakun wutan lantarki da kuma sata kayayyaki masu muhimmaci.

A watan Oktoban da ya gabata, barayin sun lalata muhimmin layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Kaduna mai karfin 330kV da ke samarwa jihohin Kano da Kaduna, da kuma wani layin da ke samar da Bauchi da Gombe da sauran sassan arewa maso gabas wuta.

Wannan lamari dai ya haifar da bacin rai na tsawon wata guda a jihohi 17 cikin 19 na arewacin ƙasar. Bayan gyare-gyaren, gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yi kira da a samar da wutar lantarki masu zaman kansu ga jihohin domin tabbatar da ingantacciyar wutar lantarki a yankin.

Jihohin sun hada da Neja da Kwara da Kaduna da Kano da Jigawa daGombe da Katsina. Sauran sun hada da Sokoto da Zamfara da Bauchi da Yobe da Borno da Adamawa da Taraba da Naija da Filato da Nasarawa da Kogi da kuma Benue.

Sai dai da yake jawabi a wurin taron da kuma bayyana nasarorin da aka samu kawo yanzu, ministan ya jaddada cewa duba da hasken rana da Allah ya albarkaci Najeriya, babu dalilin da zai sa ƙasar ba za ta iya samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp