Home General ‘Yan bindiga sun kashe mutane 28 a wasu sabbin hare-hare a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutane 28 a wasu sabbin hare-hare a Zamfara

Aƙalla mutane 28 cikin su har da masu hakar ma’adinai 20 ne ƴan bindiga suka kashe a ranar Alhamis da ta gabata a yayin wasu jerin hare-hare da suka kai ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.

Hare-haren sun auku ne da misalin ƙarfe 11 da rabi na safe akan garuruwan Gobirawa Chali, Damaga da Lugga, hare-haren da mazauna yankunan suka ce sun zo musu a bazata, inda ɗimbin yan bindiga suka kutsa garuruwan nasu a lokaci guda.

Kamfani dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani mazauna garin yana cewa ƴan bindigan sun bude wuta akan masu haƙar ma’adinai, kuma nan ne rikici ya ɓarke har mutane da dama suka mutu.

A wata sanawar da ta fitar a wannan Juma’a, ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Amnesty ta tabbatar da harin, tana mai cewa maharan sun bi gida-gida a garin Gobirawa Chali, inda suka kashe sama da mutane 20.

A garin Damaga kuwa, mutane biyar ne maharan suka kashe, ayayin da uku suka gamu da ajalinsu a garin Lugga.

Wani mazaunin Lugga ya bayyana yadda ƴan bindigar suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi a kewayen ƙauyen, kana suka yi awon gaba da dabbobi.

Rahotanni sun ce dakarun rundunar sojin ƙasar sun kawo ɗauki ba tare da ɓata lokaci ba, abin ma da ya taƙaita ɓarnar kenan.

Dakarun ƙasa da jiragen yaƙin sun shiga garin a yayin harin, inda suka yi bata – kashi, wanda ya kai ga mutuwar ɗimbin maharan.

Waɗannan hare-hare su na nuni da yadda ake cigaba da samun matsalar  tsaro a jihar Zamfara, inda ƴan bindiga suka addabi ƙauyuka da dama, duk kuwa da aikin da sojoji ke yi a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp