Hukumomi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da tashin gobara a rumbun adana makamai da ke barikin sojoji da ake kira ‘Giwa Barrack’ a birnin Maiduguri.
Gobarar ta janyo fashewar abubuwa tare da haddasa fargaba a tsakanin al’umma a Maiduguri saboda ƙara mai ƙarfin gaske da aka ji a ƙwaryar birnin da kewaye.
Mazauna birnin Maiduguri sun shiga zulumi sakamakon tashin gobarar, inda galibin jama’a suka zaci cewa ‘yan Boko Haram ne suka kai hari.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hukumar da ke kula da kashe gobara ta jihar Borno a cikin wata sanarwa, ta ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10 da rabi na dare a ranar Laraba, inda ta lalata rumbun adana makamai na barikin sojojin.
Daga bisani ‘yan kwana-kwana sun samu nasarar kashe gobarar.
Binciken farko da hukumomi suka yi kan musababbin tashin gobarar, ya gano cewa tsananin zafi a Maiduguri na da alaƙa da tashin gobarar.
A shekara ta 2014 ne, ƙungiyar Boko Haram ta kai hari a barikin sojoji na Giwa lamarin da ya janyo hasarar rayuwa da dama.











