Home General A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu

A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu

Hare-haren da aka kai a Jihar Filato sun hallaka aƙalla mutum 20 a wannan makon, in ji majiyoyin gwamnati da ƙungiyoyin agaji a ranar Laraba.

Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin.

Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar Mangu a ranar Litinin da Talata, sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da ake kyautata zaton sun fara ne yayin da mutane ke aikin haƙar ma’adinai a yankin da ke da arzikin Tin, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, da ya shaida wa Kamfanin dillancin labarai na AFP.

“Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zauna a Jihar Filato — waɗanda mafi yawansu Kiristoci ne — kan rikicin mallakar fili da albarkatun ƙasa.” in ji shugaban.

Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa a yankin sau da yawa na da nasaba da bambancin ƙabila da addini, wanda ke haifar da hare-haren ramuwar gayya marasa kakkautawa.

“Watanni da suka wuce, wasu mazauna yankin na aikin haƙar ma’adinai, sai aka kai musu hari da adduna, kodayake babu wanda ya mutu a harin farko.”

“Amma bayan jerin ramuwar gayya da martani, an kai hare-hare uku a ranar Litinin da Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20”, in ji Bala

Wani jami’in Red Cross ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu cikin sa’o’i 24 a harin Chinchin, yana mai cewa adadinsu na iya kai wa 21.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp