Home General Bello Turji ya kashe ƴan sa-kai sama da 40 a Zamfara

Bello Turji ya kashe ƴan sa-kai sama da 40 a Zamfara

Rahotannin na bayyana cewa guda cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi.

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya.

An dai yi wa jami’an da ke tafiya a cikin motoci biyu da babura kwanton baunar ne a yankin wanda ya shafe mako biyu babu sabis din waya saboda aikin da sojoji suke a ciki.

Wata majiya a yankin ta tabbatar wa Aminiya cewa harin ya daga musu hankali matuka kuma an shirya shi yadda ya kamata.

Majiyar ta ce, “An mamaye su. Bello Turji da yaransa sun kashe mutum 40 daga cikinsu sannan suka kwace ababen hawan da suke kai.

“Turji ya ji dadin harin sosai musamman saboda Bashar Maniya na cikin wadanda aka kashe, wanda tun a baya dama babban abokin hamayyarsa ne kafin ya tuba daga ta’addancin,” in ji majiyar.

A cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Bello Turji yana murna tare da nuna gawarwakin mutanen, ciki har da ta Bashar Maniya, yana rera wakokin cin nasara.

“Wannan ce gawar Kwamandan da ya jagoranci harin,” kamar yadda aka jiyo Turjin yana bayyanawa a cikin bidiyon.

Daga bisani dai an kwaso gawarwakin mutanen tare da gudunmawar sojojin sama, yayin da wadanda suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti.

Wani jami’in tsaro da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi da abin takaici da za a iya kauce masa matukar ana aiki tare tsakanin jami’an tsaro da mutanen gari.

Bayanai dai sun nuna gabanin kisan mayakan, an kashe ’yan bindiga yaran Bello Turji sama da 30 a wata ba-ta-kashi da aka yi tsakanin yaran Turjin da na Maniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp