Rahotannin daga Najeriya na bayyana cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi babu kakkautawa ya haifar da ambaliya a ƙananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu na jihar Adamawa, inda rahotanni suka ce an samu rasa rayukan aƙalla mutum 23 da rugujewar gidaje.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ruwan sama kamar kamar da bakin kwarya, wanda aka fara tun kafin wayewar gari kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, ya yi barna sosai ga al’ummomin yankin.
unguwannin da lamarin ya fi shafa sun hada da Yola Bye Pass da Sabon Pegi da Yolde Pate da Modire, saboda yadda gidaje suka ruguje, tare da lalata filayen noma da hanyoyin mota, lamarin da ya hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa.
Rahotanni na cewa mutane da dama sun mutu, yayin da ƙanan yara da dama suka bace, inda har yanzu ake ci gaba da aikin ceto.












