Home Labarai zamu hallaka Da;iban da ke hannun mu matukar baku biya Fansa ba...

zamu hallaka Da;iban da ke hannun mu matukar baku biya Fansa ba – ‘Yan Bindiga

Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun ƙwarewar a aikin lauya da aka sace a jihar Benue sun ce idan ba a biya kuɗin fansa ba, za su kashe su.

An sace ɗaliban ne a ranar 26 ga watan Yulin a hanyarsu ta zuwa makarantar domin samun horo da ke Yola a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashi.

jaridar ta Punch ta ruwaito daga wata majiya cewa masu garkuwar sun ƙara kuɗin fansar daga dala 13,110 zuwa dala 32,688 kan kowane ɗalibi, sannan suka yi barazanar kashe ɗaliban matuƙar ba a biya kuɗin ba.

“Sun ce idan ba mu kawo kuɗin ba, za su kashe su, sanan sun gargaɗe mu kada mu saka jami’an tsaro a maganar.”

Kakakin runduar ƴansandan jihar Adamawa, Yahaya Suleiman ya ce suna aiki tare da rundunar jihar Benuwai domin ceto ɗaliban.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp