Gwamnatin Najeriya ta cire wajibcin cin darasin lissafi cikin sharuɗaɗan samun gurbin karatu a jami’a ga ɗaliban da za su karanci kwasa-kwasan da na na kimiyya ba.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar ilimin ƙasar ta fitar ta ce daga yanzu ɗaliban da ke son karanta kwasa-kwasan da ba su da kusanci da kimiyya ko fasaha ba, cin darasin lissafi a sakandire bai zame musu wajibi ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kwasa-kwasan sun haɗa da nazarin ilimin harsuna da zane-zane da nazarin wasannin kwaikwayo da kaɗe-kaɗe, amma dole sai sun ci darasin Ingilishi a sakandire.
Sai dai sanarwar ta jaddada wajibcin darasin lissafin ga sauran kwasa-kwasan da suka shafi kimiyya da fasaha da nazarin zamantakewa.
Ma’aikatar ta ce ta ɗauki matakin ne domin ɗalibai da dama su riƙa samun damar shiga jami’a.
”Matakin zai samar da ƙarin guraben karatu 300,000 a kowace shekara, domin rage yawan ɗaliban da ba sa samun guraben karatu, tare da ƙarfafa sana’o’in dogaro da kai”, in ji sanarwar.











