Home Labarai Ma’aikatan lantarki sun yi barazanar katse wuta a faɗin Najeriya

Ma’aikatan lantarki sun yi barazanar katse wuta a faɗin Najeriya

Ƙungiyar ma’aikatan lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi barazanar katse wuta a faɗin ƙasar, sakamakon zargin da take yi na cewa an kai wa ma’aikatan kamfanin rarraba lantarki na ƙasar hari.

Cikin wata sanarwa da muƙaddashin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike ya fitar, ya ce hakan ya zama wajibi ne bayan zargin wasu ƴansanda da ke aiki bisa umurnin gwamnatin jiha, sun yi wa ma’aikatan da ke aiki a cibiyar lantarki ta Egbu da ke Jihar Imo duka, da yi musu barazana da bindiga da kuma garkuwa da wasu.

A cewar sa ƴan sandan sun shiga cibiyar ne da ƙarfin tsiya, tare da lalata kayayyakin aiki da dakatar da ayyukan da ake gudanarwa, kamar yadda kafar talibijin ta channels ta ruwaito.

A cewar sanarwar, ƙungiyar ta riga ta bai wa mambobinta umurnin katse samar da lantarki a jihar Imo har sai wani lokaci.

Ta kuma yi barazanar katse aiki a faɗin Najeriya har sai hukumomi sun ɗauki matakan gaggawa na tabbatar da tsaron ma’aikatan lantarki a faɗin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp