Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, jam’iyyar ta ce matakin da Gwamna Yusuf ya ɗauka tamkar cin amanar al’ummar jihar Kano ne, wanɗanda a cewarta, sun kaɗa masa ƙuri’a ne sakamakon daɗewar da ya yi yana tare da tafiyar siyasar Kwankwasiyya.
Read Also:
”Muna matuƙar takaicin yadda Gwamna Abba, mutumin da al’ummar Jihar Kano suka damka wa al’ummar Jihar kan karfin biyayya da sadaukarwar da ya yi na tsawon shekaru da dama da ya yi wa tafiyar Kwankwasiyya, a yanzu ya zaɓii ya ci amanar da aka miƙa masa.” in ji sanarwar
Ta kuma ƙara da cewa ”Wannan mataki na iya mayar da jihar hannun waɗanda suka daɗe suna adawa da ci gabanta da muradun al’ummarta.”
Jam’iyyar NNPP ta buƙaci magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, su kuma yi taka-tsan-tsan kan duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma a siyasance ko kuma ta da zaune tsaye.












