Ba a nemi izinin majalisa ba kafin kai harin Amurka a Najeriya – Sanata Ningi

Sanata Abdul Ahmed Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya bayyana damuwa kan yadda Amurka ta kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto ba tare da neman izini ko tuntuɓar majalisar dokokin ƙasar ba kafin ta kai harin.

Sanatan ya ce “hakan ya saɓa wa ikon ƙasar tare da karya tsarin sa ido na majalisa kan al’amuran tsaro.”

Sanata Ningi ya tayar da batun ne a zauren majalisar dattawa inda ya ce “majalisar dokoki na da rawar da doka ta tanada a harkokin tsaro da kuma shigar sojojin ƙasashen waje, amma ba a nemi ra’ayinta ba kafin kai harin.”

Ya gargaɗi cewa “barin ɓangaren zartarwa ya yanke irin wannan hukunci shi kaɗai na iya buɗe ƙofa ga wasu ƙasashe su ma su ɗauki mataki makamancin haka nan gaba.”

Biyo bayan wannan ƙorafi ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Majalisar ta shirya gudanar da zama domin tattaunawa da yan majalisa kan lamarin.

Ya ce an shirya yin bayanin tun da farko amma aka ɗage shi domin girmama marigayi Sanata Godiya Akwashiki.

Akpabio ya jaddada cewa batun tsaro ne mai matuƙar muhimmanci wanda bai dace a tattauna a bainar jama’a ba, yana mai tabbatar da cewa za a shirya zama nan ba da jimawa ba domin yi wa sanatoci bayani kan hare-haren da Amurka ta kai a ranar 25 ga Disamba 2025, wanda AFRICOM ta ce an aiwatar da shi tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya domin kai farmaki kan sansanonin ‘yan ISIS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com