Home General Kotu ta hana ƙungiyoyin ƙwadago yin yajin aiki ko zanga-zanga

Kotu ta hana ƙungiyoyin ƙwadago yin yajin aiki ko zanga-zanga

Kotun warware matsalolin ma’aikata ta ƙasa ta bayar da umarnin wucin-gadi da ke hana manyan ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya, ciki har da NLC da TUC, tare da wasu ƙungiyoyi uku, yin yajin aiki ko zanga-zangar da suka shirya farawa.

Mai shari’a Emmanuel Subilim ne ya bayar da umarnin a birnin Abuja, bayan sauraron buƙatar gaggawa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, tare da hukumar ma’aikatan babban birnin tarayya FCTA suka shigar.

Alƙalin ya umurci waɗanda ake ƙara, tare da wakilansu ko jami’ansu, da su dakatar da duk wani nau’i na yajin aiki ko zanga-zanga har zuwa lokacin da za a saurari buƙatar da aka gabatar.

Haka kuma, kotun ta umurci hukumomin tsaro da ke cikin ƙarar da su tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda, tare da hana duk wani rikici a Babban Birnin Tarayya.

Lauyan da ke wakiltar minista Wike da FCTA, Ogwu Onoja, ya shaida wa kotu cewa shugaban ƙungiyar ƙadago ya fitar da wata sanarwar tattara mambobi da ƙungiyoyin haɗin gwiwa domin shirya babbar zanga-zanga a ranar 3 ga Fabrairu, lamarin da ya ce ya saɓa wa umarnin kotu.

Sanarwar, wadda shugabannin ƙungiyoyin biyu suka rattaɓa wa hannu, ta umurci ma’aikatan da ke yajin aiki da su ci gaba, bisa hujjar cewa lauyansu, Femi Falana, ya shigar da ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin wucin-gadin da kotu ta yanke.

Haka kuma, an ce haɗakar ƙungiyar ƴan ƙwadago ta JUAC ta fitar da wata sanarwa da ke umartar dukkan ma’aikata da su ci gaba da yajin aikin, matakin da ɓangaren masu ƙara suka ce na iya haddasa rushewar doka da oda a Babban Birnin Ƙasa.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp