Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar soji zuwa sassan jihar Kwara, bayan mummunan harin da ya yi sanadiyyar kisan gomman mutane a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar.
Shugaba Tinubu a wata sanarwa da kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar ranar Laraba da dare ya kuma naɗa kwamandan da zai jagoranci rundunar sojin da za a tura jihar Kwara, wadda za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya da aka yi wa laƙabi da ‘Operation Savanna Shield’.
Gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan harin da aka kai wa ƙauyen Woro, inda rahotanni ke cewa an tattara gawarwakin mutane 78 da maharan suka kashe.
a wata ganawa da kafar yada labarai ta BBCHausa ta yi da Hon Sa’idu Baba Ahmed, ɗan majalisar dokokin jihar Kwara, ya shaidawa cewa sun yi jana’izar sama da mutane 70 daga cikin waɗanda maharan suka kashe.
Ya ce ”abin da dai na gani, waɗanda muka yi wa sallah, mutum 78 ne amma akwai waɗanda aka ƙone a cikin gidajensu, ba mu san adadin su ba tukun. An hallaka mutum zai kai 170.”
Hon. Baba Ahmed ya kuma ce maharan ”sun wuce da mata 38,” daga ƙauyukan da suka kai wa hari.











