Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai kan sansanin sojin Auno a Borno, sannan suka kaddamar da harin ramuwar gayya wacce ta lalata kayan yaƙi da dabarun ‘yan ta’addan.
Rundunar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarai.
Sanarwar ta ce “A daren 5 ga Fabrairun 2026, mayaƙan ISWAP sun kai hari kan wani sansanin sojoji amma Sojojin sun dakile harin cikin tsari da ƙwarewa.”
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Bayan daƙile harin, a ranar 9 ga Fabrairu, sojojin tare da hadin gwiwar dakarun sa kai ta CJTF suka ƙaddamar da samame ta ramuwar gayya a kan mayaƙan ISWAP ɗin a layin Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga.
A yayin samamen, sojojin sun kashe mayaƙan Iswap 16, yayin da sauran suka tsere da raunuka masu tsanani.
Haka kuma, sojojin sun ƙwato fiye da kekuna 20 da kayayyakin yaƙi da dama da makamai da sauran kayan amfani na ‘yan ta’adda.
Sojojin sun kuma kama wasu mutane da ake zargin suna tura ƙwayoyi da sauran kayan aiki don taimakawa ayyukan ISWAP a yankin Bukarti.












