Home General Waye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton ‘Yansandan Najeriya

Waye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton ‘Yansandan Najeriya

An haifi Tunji Disu a yankin Lagos Island, dake Jihar Lagos, ranar 13 ga Afrilu, 1966. Ya shiga Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya a ranar 18 ga Mayu, 1992, inda ya fara aikin a sassa daban-daban na gudanarwa, bincike da yaki da manyan laifuka.

A tsawon shekarun aikinsa na farko, Disu ya rike mukamin baturen ‘Yansanda (DPO) a yankuna da suka hadar da Ago Iwoye (Jihar Ogun), Ikare da Owo (Jihar Ondo), da kuma Elimbu da Elelenwo (Jihar Rivers). A wadannan wurare, ya jagoranci ayyukan tsaro, binciken laifuka da kula da zaman lafiya a matakin kananan hukumomi.

Bugu da kari, ya taba zama Shugaban Rundunar Special Anti-Robbery Squad (SARS) da sashen yaki da garkuwa da mutane a Jihar Rivers. Haka kuma, ya jagoranci SARS a jihohin Ondo, Oyo da Rivers. Ya kuma yi aiki a matsayin Mataimaki na Biyu (2IC) a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na Jihar Rivers.

A shekarar 2005, Disu ya jagoranci tawagar farko ta ‘yan sandan Nijeriya a karkashin aikin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Sudan (AMIS). A lokacin da yake Darfur, an nada shi a matsayin Mukaddashin Babban Hafsan Tawaga (Acting Chief of Staff) har zuwa dawowarsa Nijeriya a shekarar 2006. Wannan ya sami kwarewa a fannin tsaron kasa da kasa da gudanar da tawaga a yanayin rikici.

Daga 13 ga Yuni, 2015 zuwa Agusta 2021, Disu ya jagoranci Rundunar Rapid Response Squad (RRS) ta Jihar Lagos; A wannan lokaci, ya aiwatar da sauye-sauye masu tarin gaske kama daga tsarin aiki da alakar jami’ai da jama’a.

Ya lakaba wa jami’ansa suna “The Good Guys” domin karfafa dabi’ar aiki cikin mutunci, ladabi da bin ka’idojin doka. Rundunar ta rungumi tsarin aikin hadin gwiwa da al’umma (community-based policing), tare da mayar da hankali kan magance lafi kafin aikatashi (rigakafi), tattara bayanan sirri da kuma amfani da fasahar taswirar laifuka (crime mapping) da dabarun hot-spot policing.

Wadannan matakai sun haifar da rage aikata laifuka da kuma karuwar ganin motocin sintiri a wuraren da ake yawan samun matsaloli a fadin Lagos.

Rahotanni sun nuna cewa RRS ta samu karbuwa daga al’ummar Lagos, inda jami’anta ke taimakawa direbobin motocin da suka lalace da kuma agazawa wadanda suka ji rauni a hadurra. A lokacin dokar kullen COVID-19 a 2020, jami’an rundunar sun kai wata mata mai nakuda asibiti domin ceton rayuwarta.

Disu ya yi aiki a matsayin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP), Sashen Ayyuka, a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja.

A ranar 2 ga Agusta, 2021, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a wancan lokaci, Usman Alkali Baba, ya nada shi a matsayin Shugaban Intelligence Response Team (IRT), mukamin da a baya Abba Kyari ya rike.

A watan Yuli 2022, Sufeto Janar ya yaba wa tawagar FIB-IRT karkashin jagorancinsa bisa nasarorin da suka samu, ciki har da cafke wata kungiyar masu damfarar asusun bankuna na daidaikun mutane da kamfanoni.

A watan Maris 2023, Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta kara masa girma zuwa mukamin Kwamishinan ‘Yan Sanda (CP), matakin da ya tabbatar da karuwar amincewa da kwarewarsa a fannin tsaro.

Baya ga aikin tsaro, Disu gogaggen dan wasan Judo ne mai bakin bel mataki na uku (3rd Dan). Tun bayan fara wasansa a 1986, ya lashe lambobin yabo da dama.

A ranar 31 ga Yuli, 2022, ya samu lambar azurfa a gasar U.S. Open Judo Championship karo na 33 a ajin tsofaffi (veteran division) na rukunin kasa da kilo 100.

A lokacin zanga-zangar EndSARS ta 2020 kan zargin cin zarafin jama’a, rahotanni sun bayyana cewa Disu, a matsayinsa na shugaban RRS a wancan lokaci, ya bayar da motocin daukar marasa lafiya na rundunarsa domin taimakawa masu zanga-zanga da ke bukatar kulawar gaggawa.

A lokacin nadinsa, an ruwaito cewa an haife shi a ranar 17 ga Afrilu, 1960, sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, ya karyata rahoton tare da tabbatar da cewa shekarar haihuwarsa ita ce 1966.

A karkashin jagorancinsa, Rundunar RRS ta Lagos ta samu kyautar mafi kyawun rundunar yaki da laifi a Yammacin Afirka daga Security Watch Africa a 2016.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓe
X whatsapp